Bayanai kan cutar Daji a duniya

Hukumar lafiya ta duniya tare da hadin gwiwar cibiyar binciken cutar kansa ko daji ta kasa da kasa sun ware ranar hudu ga watan Fabrairu na kowace shekara a matsayin ranar yaki da cutar.

Taken ranar ta wannan shekarar shi ne " Za mu iya, kai ma haka."

A wannan rana ana bukatar kowa ya bayar da gudunmawarsa domin yaki da cutar a fadin duniya.

Akwai sana'oi da dama wadanda ke jefa masu yinsu cikin hadarin kamuwa da cutar, ciki har da aikin kafinta.