Al-Shabab ta karbe garin Merca a Somalia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mazauna garin sunce sun ga 'yan Al-Shabab na sunturi a kan kuma sun fara wa'azi

Kungiyar masu fafutukar Islama ta Al-Shabab ta karbe iko da birnin Merca mai tashar jiragen ruwa a Somalia, a cewar mazauna garin.

Birnin wanda bai wuce nisan kilomita 70 daga babban birnin kasar ba, Mogadishu, ya kasance gari mafi girma da ke karkashin ikon kungiyar.

Hakan ya faru ne bayan dakarun Afrika da ke rike da Merca tsawon shekaru uku da rabi sun janye daga birnin da safiyar ranar Juma'a.

Gwamnan yankin Lower Shabelle, Ibrahim Adam, ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa al-Shabab ta karbe iko da garin cikin ruwan sanyi.

Masana dai sun ce karbe birnin Merca wani babban koma baya ne, a fadan da dakarun Afrika suka shafe shekaru goma suna yi da Al-Shabab.