Al-Shabab ta yi babban kamu a Somalia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan Al-shabab suna ta'asa a Somalia

Kungiyar al-Shabab ta kwace wani muhimmin gari mai tashar jirgin ruwa da ake kira Merca.

Garin Merca, mai tazarar kilomita 70 daga Mogadishu babban birnin kasar, shi ne gari mafi girma da kungiyar ta kwace daga jami'ain tsaro.

Dakarun kungiyar AU ne ke iko da gari na tsawon shekara uku da rabi, kafin su fice da safiyar ranar Juma'a.

Hakan babban koma-baya ne ga dakarun kungiyar AU din wacce ta shafe fiye da shekaru goma tana fafatawa da kungiyar al-Shabab.

Gwamnan lardin Lower Shabelle, Ibrahim Adam ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa kungiyar al-Shabab ta kwace garin cikin ruwan sanyi.