Gaskiya ta yi halinta — Assange

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Assange ya shafe shekaru a ofishin jakadancin Ecuador

Mutumin da ya kirkiri shafin intanet mai kwarmata bayanai na Wikileaks, wato Julian Assange, ya yi marhabin da rahoton wani kwamitin bincike na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya ce Biritaniya da Sweden sun tsare shi ba bisa ka'ida ba.

A cewarsa hakan wata babbar nasara ce.

Mista Assange ya ce rahoton ya faranta masa rai, kuma hujja ce ta cewa tsare shi ya haramta.

Da yake magana daga ofishin jakadancin Ecuador a Landan ta hanyar sadarwa ta bidiyo, ya kara da cewa kamata ya yi a kyale shi ya yi tafiyarsa.

Sakataren harkokin wajen Biritaniya, Phillip Hammond, ya bayyana hukuncin da cewa abin dariya ne.

"Julian Assange mutum ne dake gujewa shari'a a ofishin jakadancin Ecuador. Zai iya fitowa bakin titi duk lokacin da ya so, mu ba tsare shi ba," in ji Hammond.