'Ba za mu rage darajar naira ba'

Image caption Shugaba Muhammadu Buhari a hirarsa da Mansur Liman na BBC, a lokacin da shugaban ya kai ziyara Landan.

Shugaba Buhari ya ce ba zai rage darajar kudin kasar, Naira, ba, yana mai cewa babu wata shaida da ke nuna cewa tattalin arzikin kasar zai bunkasa idan aka rage darajar kudin.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida wa BBC cewa ba zai yarda 'yan damfarar da ke amfani da sunan Boko Haram su yaudare shi ba.

Shugaban ya yi wadannan kalaman ne a hirarsa da BBC a London, bayan ya hallaci taron neman agaji ga 'yan gudun hijirar Syria.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne bayan da wasu mutane ke fitowa suna cewa za su shiga tsakanin gwamnati da Boko Haram domin a saki 'yan matan Chibok sama da 200 wadanda kungiyar ta sace a shekarar 2014.

Shugaban na Najeriya ya kara da cewa tattalin arzikin kasar ya fada mawuyacin hali ne saboda faduwar da farashin man fetur ya yi a kasuwannin duniya.

Sai dai ya ce gwamnatinsa tana duba wasu hanyoyin domin samun kudin-shiga.

Shugaba Buhari ya ce ba zai rage darajar kudin kasar, Naira, ba, yana mai cewa babu wata shaida da ke nuna cewa tattalin arzikin kasar zai bunkasa idan aka rage darajar kudin.

Ga kadan daga cikin hirar tare da shugaban Sasashen Hausa na BBC Mansur Liman

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti