CBN zai ba 'yan kasuwa da manoma bashi

Gwamnan bankin CBN Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shirin na CBN zai taimakawa masu kananan sana'o'i, da 'yan kasuwa da manoma.

A Nigeria wasu kungiyoyi masu zaman kansu na tattaunawa a kaduna tare da kungiyoyin manoma, da 'yan kasuwa da sauran wasu masu sana'oi a kasar.

Domin wayar musu da kai a bisa hanyoyin samu da kuma sarrafa Basussuka daga Bankunan kasar, musamman babban bankin Nigeria CBN.

Kungiyoyin dai na shiga tsakani ne domin ganin manoma da 'yan kasuwa a kasar sun ci moriyar kudaden da babban bankin ya ware domin bunkasa kasuwanci da masana'antu.

Akasari dai 'yan kasuwa da manoma a Nigeria kan kwana kan Dami a sanadiyyar rashin sanin dabarun samu da kuma sarrafa basussuka daga bankuna.

Bangaren Noma dai ya fuskanci koma baya a Nigeria, inda yawancin 'yan kasar suka dogara da kayan abinci da ake shigo da su daga kasashen waje.

Amma a yanzu gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta lashi takobin dawo da martar Noma a kasar, ta yadda al'umar Nigeria za su rage dogaro da kayan abinci na kassahen ketare.