Paparoma zai gana da shugaban Cocin Orthodox

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Manyan shugabannin biyu na Kiristoci

Nan da mako guda za a yi ganawa ta farko tsakanin jagoran Cocin Katolika da shugaban Cocin Orthodox ta Rasha.

Fadar Paparoman ta Vatican ta ce a Cuba za a yi ganawar tsakanin Paparoma Francis da Patriarach Kirill.

Wani babban malamin Cocin Orthodox ya ce ganawar lamari ne mai muhimmanci.

Wannan ce dai ganawa ta farko da za a yi tsakanin bangarorin biyu tun bayan da al'ummar Kirista ta dare a karni na 11.

Masharhanta sun ce ganawar muhimmin mataki ne na dinke barakar da ke tsakanin bangaren yammacin duniya na al'ummar Kirista da na gabashin duniya.