Za a tuhumi Bukola Saraki

Image caption Sanatoci na raka Saraki a zaman kotu

Kotun Kolin Najeriya ta amince kotun kula da da'ar ma'iakata ta ci gaba da tuhumar da take yi wa shugaban majalisar dattawan kasar, Abubakar Bukola Saraki, bisa zargin yin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Sanata Saraki ya kai kotun kula da'ar ma'aikatan gaban kotun kolin ne inda yake so ta hana ta tuhumarsa, yana mai cewa ba ta da hurumin sauraren kara a kansa.

Sai dai kotun kolin ta ce kotun kula da da'ar ma'aikatan tana da hurumin yi masa shari'a.

A martanin da ya mayar, Sanata Abubakar Bukola Saraki ya bayyana takaicinsa game da hukuncin na kotun koli, inda ya jaddada cewa zai wanke kansa a shari'ar da ke tafe.

Saraki ya kara da cewa gaskiya za ta yi hallinta.

Kotun kula da da'ar ma'aikatan dai tana tuhumar shugaban majaliasar dattawan ne bisa zarge-zarge goma sha uku -- cikin su har da zargin kin bayyana kadarorin da ya mallaka, a lokacin da yake gwamnan jihar Kwara.

Tun da fari dai, sai da Mista Saraki ya kai kotun kula da da'ar ma'aikatan gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja don ta hana a tuhume shi, amma bai yi nasara ba.