Mahaifiyar Shugaba Assad ta rasu

Bashar al-Assad Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Anissa Makhloof al-Assad ta dade ta na fama da rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

Kafar Yada labaran gwamnatin Syria ta ce mahaifiyar Shugaba Bashar al-Assad ta rasu a birnin Damascus tana da shekaru 86.

Anissa Makhlouf al-Assad ita ce matar marigayi Tsohon Shugaban kasar Hafiz Assad, wanda suke da 'ya'ya biyar tare.

Sai dai ba ta cika fitowa cikin jama'a ba, kuma ba kasafai kafofin yada labarai suke bada labarinta ba.

Kamfanin dillacin labaru na Syria SANA bai yi wani karin bayani ba dangane da rasuwar ta.

Amma masu aiko da rahotanni sun ce ta shafe shekara da shekaru tana jinya, kuma a wasu lokutan ta kan je kasar Jamus neman magani har zuwa shekarar 2012, a lokacin da Tarayyar Turai ta sanya ta cikin fitattun 'yan Syria da aka haramtawa tafiya.