An kai hari a wasu kauyukan Maiduguri

Rahotanni daga jihar Borno a Najeriya sun ce wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kaddamar da hare-haren a wasu kauyuka da ke kusa da Maiduguri.

Bayanai sun ce mayakan sun halaka mutane hudu a hare-haren da suka kai a kauyukan Malari da kuma Mairi masu tazarar kilomita 20 daga Maiduguri.

Wani mazaunin kauyen Mairi ya shaida wa BBC cewa 'yan Boko Haram din sun kai hare-haren ne a ranar Juma'a da yamma inda suka kona gidaje da dabbobi masu yawa.

Wannan harin shi ne na baya-bayanan da 'yan Boko Haram suka kai a daidai lokacin da hukumomi a Najeriya ke ci gaba da ikirarin samun galaba a kan kungiyar.

Ga rahoton Raliya Zubairu:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti