Korea ta Arewa ta harba makamin roka

Makamin Nukiliyar Korea ta Arewa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ba wannan ne karon farko da Korea ta Arewa ta yi gwajin makamin Nukiliya ba.

Korea ta Arewa ta harba makamin roka mai cin dogon zango, da ya saba da dokokin Majalisar Dinkin Duniya abinda ya janyo Allawadai daga kasashen duniya.

Kafar yada labaran Korea ta Kudu ta ce makamin rokar ya wuce ta sararin samaniyar kasar Japan ta tsuburin Okinawa.

Amma Kasashen yammacin duniya sun ce makasudin yin hakan shi ne gwajin makami mai linzami, inda suka zargi Pyongyang da kokarin kera makamin Nukiliya mai cin dogon zango da zai isa har Amurka.

Kasashen Amurka da Japan da Korea ta Kudu sun bukaci yin taron gaggawa na kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a yau Lahadi don tattauna batun.

Ga rahotan da Badariyya Tijjani Kalarawi ta hada mana

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti