Yan Syria dubu 35 sun kwarara zuwa Turkiya

Kan iyakar Turki

Turkiya ta ce tsawon kwanaki biyu da suka wuce yan Syria kimanin dubu 35 sun yi dandazo a kan iyakarta bayan da suka guje wa luguden wuta da dakarun gwamnati wadanda ke samun goyon bayan Rasha ke kai wa.

Ba a bar yan gudun hijirar sun tsallaka kan iyakar ba.

Wani gwamnan lardi yace an basu abinci da matsuguni a yankin da ke cikin Syria, a saboda haka babu bukatar barinsu su shiga cikin Turkiya.

Mutanen sun bar muhallan su ne sakamakon farmaki ta sama Rasha ke kai wa wanda ya taimakawa sojojin Syria dannawa arewacin birnin Aleppo.

Tun da farko fadar White house ta Amurka ta ce, kwararar dubban 'yan gudun hijirar Syria zuwa kan iyakar Turkiyya ya haddasa gagarumar matsalar agaji wacce za ta iya tabarbarewa.