Ana ci gaba da aikin ceto a Taiwan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Girgizan kasar ta faru ne da tsakar dare a lokacin da mutane ke barci. Dogon ginin mai hawa 17 ya binne mutane da yawa.

Masu aikin ceto a kasar Taiwan na ci gaba da neman mutanen da buraguzan wani dogon gini ya danne a yayin girgizar kasar da ta faru a tsibirin a safiyar yau Asabar.

Akalla mutane 12 ne suka mutu yayin da sama da 500 suka jikkata, kimanin 200 kuma aka zakulo su da rai, a lokacin da ginin mai hawa 17 ya ruguje a garin Tainan.

Mazauna garin sun yi amfani da tsani da kuma wasu kayan aiki a kokarinsu na ceto wadanda ginin ya binne.

Girgizar kasar mai karfin 6.4 ta faru ne da tsakar dare, a yayin da mutane da yawa ke barci.