Harin gurneti ya hallaka mutane hudu a Burundi

Hakkin mallakar hoto AP

Wani harin gurneti da aka kai a wata mashaya a Bujumbura babban birnin Burundi ya hallaka mutane hudu.

Cikin wadanda suka rasu har da wani karamin yaro da ke tallar dafaffen kwai.

Babu wanda ya baiyana daukar alhakin kai harin.

A ranar Juma'a kungiyar yan tawaye ta FORUBE ta yi ikrarin cewa ita ke da alhakin hare hare da dama wanda ya hallaka mutane biyar da suka hada da jami'an tsaro.

Mutane kimanin 400 suka rasu a hare hare tun daga watan Aprilu bayan da shugaban Nkurunziza ya kudiri aniyar yin tazarce karo na uku a karagar mulki.

Kungiyar tarayyar Afirka tana kokarin shawo kan shugaban ya amince a tura dakarun kiyaye zaman lafiya na AU zuwa kasar amma ya ki.