Zaman dar dar ya ragu a Kidal

Hakkin mallakar hoto

Rahotanni daga Kidal a arewacin Mali sun ce zaman dar dar ya ragu matuka bayan da aka sanya hannu a kan wata yarjejeniyar sulhu tsakanin tsoffin yan tawayen Abzinawa da ke mulkin garin da mayaka masu goyon bayan gwamnati wadanda suka isa garin a makon da ya wuce.

Tun da farkotsoffin yan tawayen MNLA sun bukaci janye makayakan masu goyon bayan gwamnati wadanda aka fi sani da Platform.

Yanzu sun sanya hannu akan yarjejeniya wadda a karkashinta Platform din ta amince ta rage mayakanta a garin yayin da a waje guda kuma za a bata ikon kula da wani yanki na Kidal.