Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi Korea ta Arewa

Kaddamar da Roka a kasar Korea ta Arewa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kaddamar da Roka a kasar Korea ta Arewa

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ce zai aza sabon takunkumi kan kasar Korea ta Arewa, bayan da ta harba roka mai dogon-zango.

Kwamitin sulhun ya yi Allah wadai da matakin na Korea ta Arewar, tare da bayyana shi a matsayin mai hadarin gaske.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce lallai ne Pyongyang ba za ta ji da dadi ba, don zata aza mata sabon takunkumi.

Amma kuma kasar China ta ce muddin matakan suka tsaurara kasar Korea ta Arewan zata shiga wani hali.

Pyongyang din dai ta ce kaddamar da rokar, daya daga cikin shirye-shiryenta ne na ayyukan sararin samaniya, amma sauran kasashen sun yi amanna tana yunkuri ne ta hada makaman nukiliya masu cin dogon zango.