'Koriya ta Arewa za ta gwada nukiliya ne'

Hukumar leken asiri ta Koriya ta Kudu ta ce Koriya ta Arewa na shirin yin gwajin makamin nukiliya a karo na biyar.

Ta ce Koriya ta Arewar na wannan shirin ne bayan da ta harba roka mai nisan-zango -- lamarin da ya saba wa kudurorin Majalisar Dinkin Duniya.

Wani rahoton majalisar dokokin Koriya ta Kudun ya ce hukumar leken asirin ta ce Pyongyang na da na'urar harba makamai masu lizami da ke iya ketara nahiyoyi.

Da farko dai a ranar Lahadin nan Koriya ta Arewan ta ce ta yi nasarar harba roka a sararin samaniya, amma masu adawa da ita sun ce tana shirin yin gwajin makamin nukiliya ne.

Makwabtan Koriya ta Arewan da kasashen Yamma sun yi suka sosai akan harba rokar, koda yake dai China ta bayyana rashin jin dadi ne kawai.