'Za mu yi atisayen sojoji'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sojojin Amurka a yayin da su ke bakin aiki.

Koriya ta Kudu ta ce za ta yi atisayen sojoji mafi girma ita da Amurka a matsayin martani ga barazanar Koriya ta Arewa.

Za a yi atisayen sojojin ne a watannin Maris da Afrilu tare da sojojin Amurka na musamman.

Koriya ta Kudu da Amurka za kuma su soma tattaunawa a kan girke wata na'ura mai kakkabo makami mai lizami a bakin gabar Koriya.

Ryu Je-Seung, wani babban jami'in ma aikatar tsaro ta kasar ya ce, za a yi amfani da na'urar ce a kan Koriya ta Arewa.

A baya, China ta nuna adawarta ga kafa irin wannan na'ura a yakin.