Turkiya na cikin tsaka mai wuya- Erdogan

'Yan gudun hijirar Syria a kan iyakar Turkiyya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan gudun hijirar Syria a kan iyakar Turkiyya

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yace kasarsa a shirye ta karbi dubban yan gudun hijirar Syria da suka gujewa yaki a Aleppo idan yin hakan ya zama wajibi.

Har yanzu dai Turkiyyar ta ki barin yan gudun hijirar da yawan su ya kai dubu talatin da biyar wadanda suka yi cincirindo a kan iyakar su shiga cikin kasar.

Sai dai ta na basu abinci da matsuguni a wani yanki na iyakar Syria.

Wani wakilin BBC a kusa da kan iyakar yace Turkiyya na kokarin baiyanawa duniya irin halin tsaka mai wuyar da ta sami kan ta a ciki.

A waje guda ta na matsayin mai hana kwararar dubban mutanen da ke gujewa yaki a daya bangaren kuma ta na fuskantar matsin lamba daga tarayyar turai ta hana kwararowar yan gudun hijirar.

Tuni da ma Turkiyyar ta karbi bakuncin yan gudun hijirar Syriar kimanin miliyan biyu.