Girgizar kasa: An sake ceto mutum biyu a Taiwan

Aikin ceto a kasar Taiwan
Image caption Aikin ceto a kasar Taiwan

Tawagar masu aikin ceto a kasar Taiwan ta ceto karin mutane biyu -- mace da namiji -- daga baraguzan dogon ginin da ya rufta kwanaki biyun da suka gabata, sakamakon wata girgizar kasa.

Mutane 34 ne aka tabbatar da mutuwarsu a girgizar kasar da ta abku kasar ranar Asabar, yayin da ake ci gaba da neman daruruwa da suka makale.

Wani wakilin BBC da ke kasar ya ce akwai matukar zakuwa da kuma nuna damuwa daga dangin wadanda lamarin ya rutsa da su yayin da suke zaman jira, bayan da ayyukan gaggawa na ceton da ake yi ya hana musu ketarawa cikin dakunan da suka ruguje.

Rugujewar ginin ta bankado wasu bulullukan roba --da a wasu lokutan a kan yi amfani da su a maimakon na kankare -- don rage kashe kudi.