Mata Musulmi sun yi zanga-zanga a Bosnia

Hakkin mallakar hoto AFP.Getty
Image caption Kashi 40 cikin 100 na al'ummar Bosnia Musulmai ne

Akalla mata 2,000 ne a Bosnia suka yi zanga-zanga saboda haramta musu saka hijabi a harabar kotuna da kuma wasu cibiyoyin gwamnati.

Haramcin ya shafi duk wata alama ta addini kuma an fito fili an bayyana haramcin hijabi.

Sun yi macin ne na tsawon sa'a guda a babban birnin kasar, Sarajevo.

Gwamnatin kwaminisanci ta haramta saka Hijabi a lokacin da Bosnia ke karkashin ikon Yugoslavia har izuwa shekarar 1992, lokacin da ta samu 'yancin kai.

Zanga-zangar na zuwa ne bayan da majalisar koli ta shari'a a Bosnia, ta haramta duk wata alama ta addini a cikin kotunan kasar.

Hakkin mallakar hoto Getty AFP
Image caption Masu zanga-zangar sun ce an keta hakkinsu

Wasu daga cikin matan sun rike kwalaye da ke dauke da rubutu "Hijabi 'yanci na ne".

Wacce ta shirya zanga-zangar, Samira Zunic Velagic ta ce haramcin, "Babbar barazana ce ga martabar Musulmi, da kuma akidarsu", kuma matakin yunkuri ne na hana mata Musulmai 'yancinsu na yin aiki.

Malaman addini da kuma 'yan siyasa Musulmai sun yi Allah-wadai da haramcin.

Daga cikin al'ummar Bosnia mutane miliyan uku da dubu dari takwas, kashi arba'in cikin dari Musulmai ne, a yayin da sauran galibinsu Kiristoci ne.