Kotun ICC ta yi katobara

Image caption Babbar mai shigar da kara ta kotun ICC

Kotun hukuntan manyan laifuka ta duniya ta ba da hakuri bisa wani abun kunya da aka yi lokacin saurarar karar tsohon shugaban kasar Ivory Coast, Laurent Gbagbo, inda aka bayyana sunayan shaidun da aka boye sunansu a bainar jama'a.

A ranar Juma'a ne, mai shigar da kara, ya bayyana sunayen shaidun da dama wadanda aka ba da umarnin a boye sunayensu, bayan da ya yi tunanin cewa makurofo dinsa na rufe.

Sai dai kuma an ji karara kalamansa a inda mutane ke zama, kuma tuni aka baza labarin a kafafa sada zumunta.

Yanzu haka kotun ta ba da umarnin gudanar da bincike a kan lamarin.