An gano sojan India da ran sa cikin dusar kankara

Hamadar kankara
Image caption Hamadar kankara

An gano sojan kasar Indiyan nan Lance Naik Hanamanthappa da hamadar kankara ta rufe kwanaki shida da suka gabata da ran sa.

Dusar kankara mai kaurin mita takwas ta binne Mista Hanamanthappa a yankin Siachen, tare da wasu sauran sojoji tara da duka suka riga mu gidan gaskiya.

Rundunar sojin kasar ta ce sojan na cikin mawuyacin hali, suna kuma kokarin dauke shi a ranar Talata.

Kankarar ta rufta kan wani dan karamin caji ofis na sojojin a yankin Kashmir da ke karkashin ikon India.

A kwanaki ukun da suka gabata ne dai aka fitar da tsammmanin sake samun mai sauran numfashi a wurin.