Kasuwar hannayen jarin Japan ta fadi

Kasuwar hananyen jarin Japan Nikkei Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasuwar hananyen jarin Japan Nikkei

Kasuwar hannayen jari a Japan, ta fadi kasa da kashi hudu bisa dari a yau, sakamakon faduwar farashin man petu fargabar koma bayan tattalin arzikin kasashen duniya.

Bunkasar da aka samu a fannin takardun lamunin gwamnati, da akasari ake dauka a matsayin wani ajiyar kadar ta musamman, ta ja baya a karon farko da aka taba samu.

Har ila yau kasuwar bata yi tagomashi ba a biranen Sydney, da Wellington, da kuma Manila, bayan da aka rufe kasuwannin hannayen jarin biranen New York, da London, da Paris da kuma Frankfurt a ranar Litinin.