Za a sanya wa Koriya ta Arewa takunkumi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Makamin rokan da Koriya ta Arewa ta harba

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ce zai sanya sabon takunkumi kan kasar Korea ta Arewa, bayan da ta harba roka mai dogon-zango.

Kwamitin sulhun ya yi Allah wadai da matakin na Korea ta Arewa, tare da bayyana shi a matsayin mai hadarin gaske.

Amma kasar China ta ce muddin matakan suka tsaurara kasar Korea ta Arewan zata shiga wani hali.

Korea ta Arewa dai ta ce ta kaddamar da rokar ne a matsayin daya daga cikin shirye-shiryenta na ayyukan sararin samaniya, amma sauran kasashen sun yi amanna tana yunkuri ne ta hada makaman nukiliya masu cin dogon-zango.

Tunda farko hukumar leken asiri ta Koriya ta Kudu ta ce Koriya ta Arewan na shirin yin gwajin makamin nukiliya ne a karo na biyar.