Obama zai kashe biliyan biyu kan cutar Zika

Image caption Obama ya ce zai tallafa saboda cutar Zika

Shugaba Obama zai tambayi majalisar dokoki sama da dala biliyan daya da miliyan dari takwas domin aikin gaggawa na shawo kan cutar Zika.

Kudin zai taimaka wajEn rage sauro da samar da rigakafin cutar da taimakawa mata masu karamin karfi.

Ganin abin da ke faruwa a Brazil, ana alakanta cutar Zika, wadda yawanci sauro ne ke bazata da haihuwar jarirai 'Gilu'.

Kawo yanzu dai ba a masu wanda sauro ya sakawa kwayar cutar ta Zika ba a Amurka.