Sarki Sanusi ya yi tsokaci kan darajar Naira

Mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana gamsuwarsa da kamun ludayin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

A wata hira ta musamman da BBC a wata ziyara da ya kai Africa ta Kudu, Muhammadu Sanusi na biyu ya ce, gwamnatin Shugaba Buhari ta yi kokari wajen yaki da cin hanci da rashawa da kuma yaki da kungiyar Boko Haram, kuma dukkanin wadanann abubuwa ne da za su taimakawa tattalin arzikin kasa.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, ya ce a matsayinsa na mai goyan bayan gwamnatin Muhammadu Buhari ya zama wajibi ya ba ta shawara ta duba manufarta a kan darajar Naira.

''A ra'ayi na ya kamata shugaban kasa ya sake duba shawarar da ya dauka kan batun darajar Naira, kuma matakin da babban bankin Najeriya ya dauka, ya hana mutane su shigo da dalolinsu, abin da zai taimakawa tattalin arzikin kasar," in ji Sarki Sanusi.

Sarkin ya kuma jinjinawa Shugaban kasar a matakan da ya dauka wajen yaki da rashawa da kuma gyara da ake yi a bangaren man fetur.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti