'Ana azabtar da fararen hula a Syria'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana lakadawa mutane duka

Wani sabon rahoto na jami'an binciken kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya ya ce a kowane lokaci ana tsare dubban jama'a a Syria tare kuma da azabtar da su.

Rahoton ya ce azabtar da jama'a ta zama ruwan dare kuma an halaka dubban jama'a galibinsu a cibiyoyin da gwamnati ke tsare mutane.

Haka ma dai wasu mutanen sun rasu yayin da suke tsare a hannun 'yan adawa.

Rahoton wanda kacokan ya dogara daga bayanai na mutanen da aka yi hira da su da kuma shaidu za'a mika shi ga majalisar kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya nan gaba a wannan watan.

A cewar rahoton na majalisar dinkin duniya, an tsare dubun dubatan fararen hula 'yan Syria wadanda ake ganin suna goyon bayan 'yan adawa, ko kuma ba sa marawa gwamnati baya.