Mutum takwas sun mutu a hadarin jirgin Jamus

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An rufe hanyoyin da ke kusa da lamarin ya faru.

'Yan sanda a kasar Jamus sun ce mutum takwas ne suka mutu, yayin da wasu suka jikkata bayan wasu jiragen kasa sun yi taho-mu-gama a jihar Bavaria.

Rahotanni sun ce lamarin ya auku ne bayan daya daga cikin jiragen ya kauce daga kan layin-dogo, inda taragwansa suka rika cirewa, lamarin da ya sa ya daki daya jirgin.

Masu bayar da agajin gaggawa dai sun ceto mutanen da dama ta hanyar yin amfani da jirgi mai saukar ungulu.

Har yanzu ba a san yawan mutane da lamarin ya rutsa da su ba, sai dai rundunar 'yan sandan Bavaria ta wallafa a shafinta na Twitter mutane akalla mutane 100 ne suka ji rauni.

Kazalika, har yanzu ba a san takamaimai musabbabin hadarin ba.

An rufe hanyoyin da ke kusa da wurin da aka yi hatsarin, sannan an toshe layukan-dogo tsakanin yankin Holzkirchen zuwa Rosenheim.