An fasa wata tashar iskar gas a Ribas

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Akwai matatun mai da dama a yankin Niger Delta

Wasu da ake zargin masu tayar da kayar baya ne a yankin Niger Delta, sun kai hari a wata tashar iskar gas a yankin.

Kakakin sojin Najeriya a yankin, Kyaftin Lazaru Eli ya ce maharan sun kai harin ne a tashar da ke kauyen Akala a karamar hukumar Ahoada ta jihar Ribas a ranar Lahadi.

Tashar iskar gas din mallakar kamfanin Eni na Italiya ne.

Tun bayan da hukumomi a Najeriya suka bada sammacin tsohon shugaban masu tayar da kayar a baya a Niger Delta, Government Ekpemupolo, wanda ake kira Tompolo, ake samun karin hare-hare kan bututan mai a yankin.

Hukumar EFCC na zargin Tompolo da karkatar da Naira biliyan 34 a wata kwangila ta tsaro domin kare bututan mai a yankin Niger Delta, ko da yake ya musanta zargin.

Tompolo ya kasance daya daga cikin shugabannin masu tayar da kayar baya a yankin mai arzikin man fetur, kafin ya amince da yarjejeniyar afuwa da gwamnati ta yi musu a shekara ta 2009.