Erdogan ya caccaki Amurka

Image caption Erdogan ya nuna fushinsa kan Amurka

Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi kakkausan suka ga Amurka a kan goyon bayan da take yi wa mayakan Kurdawa a Syria.

Mista Erdogan ya zargi Amurka da goyon bayan kashe-kashe a yankin da kin yadda da daukar manyan kungiyoyin Kurdawa da ke Syria a matsayin 'yan ta'adda.

Kalaman Mista Erdogan na zuwa ne yayin da Turkiyya ke fuskantar matsin-lamba daga kasashen duniya na ta bude kan iyakarta ga dubban 'yan Syria da ke tserewa fadan da ake gwabzawa a lardin Aleppo.

Shi ma ministan harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius, ya soki shirin Amurka a Syria, yana mai cewa rashin tabbas dinta ya kara matsalar da ake samu.

Rahotanni daga Syria na cewa mutane fiye da dari biyar ne - ciki har da fararen hula gwammai - aka kashe tun bayan da dakarun gwamnati tare da taimakon jiragen sama na yaki, suka fara wani babban farmaki a kan lardin na Aleppo.