Idriss Deby zai tsaya takara a karo na biyar

Hakkin mallakar hoto
Image caption Idriss Deby ya yi juyin-mulki a shekarar 1990.

Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby, wanda ya fara mulki shekara 26 da suka gabata, ya ce zai sake tsayawa takara a karo na biyar a zaben da za a yi a watan Afrilu.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ambato Shugaba Deby yana cewa zai takaita wa'adin mulki a kasar bayan an sake zabensa.

A shekarar 1990 ne Shugaba Deby ya yi juyin-mulki, sannan daga bisani ya bukaci a rika gudanar da zabe a kasar.

A shekarar 2011 ne ya lashe zabensa na baya bayan nan.

Masu adawa da Shugaba Deby sun zarge shi da yin mulkin kama-karya, suna masu cewa ba a taba gudanar da sahihin zabe a kasar ba tun da ya kwaci mulki.

Mista Deby, wanda dan-barandar Faransa ne, na taka muhimmiyar rawa a yakin da ake yi da kungiyoyin 'yan ta'adda a yammacin Afirka.