Kwale-kwale ya kife a wani kogi a Jigawa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana yawan samun hadarin kwale-kwale a Najeriya

Rahotanni daga karamar hukumar Jahun a jihar Jigawa da ke Najeriya na cewa wasu mutane da dama sun rasa ransu sakamakon kifewar da kwale-kwalen su ya yi a cikin wani kogi a yankin.

Kawo yanzu dai an gano gawar mutane takwas, yayin da ake kuma ci gaba da neman wasu mutanen da dama da su ka nutse a cikin kogin.

Shugaban karamar hukumar Jahun, Alhaji Umaru Muazu ya shaida wa BBC cewa kawo yanzu ba za a iya tantance adadin mutanen da lamarin ya rutsa da su ba, har sai mutanen da aka ceto sun koma gida, sannan a iya tantance mutane nawa ne ba a gani ba.

Kawo yanzu dai ana ci gaba da aikin laluben mutanen da ake zaton sun nutse a kogin wanda kawo yanzu ba kai ga sanin adadin su ba.

Shugaban karamar hukumar ta Jahun ya ce mazauna yankin ba su da wata hanyar sufuri sai ta amfani da kwale-kwale.