Korea ta Kudu ta fara janye mutanenta daga Kaesong

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Matakin na nufin hana Korea ta Arewa samun kudaden waje.

Korea ta Kudu ta fara janye 'yan kasarta daga yankin Kaesong mai masana'antun dake Korea ta Arewa , da duka kasashen biyu ke amfana.

A ranar Laraba ne Korea ta Kudu ta sanar da cewa za ta dakatar da ayyuka a yankin na Kaesong a wani martani ga Korea ta Arewa saboda harba makamai masu dogon-zango da ta yi a baya-bayan nan.

Matakin na nufin hana Korea ta Arewa samun kudaden waje, saboda cibiyar ta Kaesong ce ke samar mata da kusan dala milyan dari a ko wace shekara, a matsayin biyan albashi ga 'yan kasar da ke aiki a masana'antun Korea ta Kudu da ke can.

Majalisar dattawan Amurka ta goyi bayan kudirin dokar azawa kasar Korea ta Arewa takunkumi mai tsauri, da gagarumin rinjaye.

Kudirin dokar na da nufin dakile yunkurin kasar na samun kudaden samar da makaman nukiliya da kuma na masu dogon-zangon da ake bukata wajen aikewa da su.

Dole dai sai kudirin ya sake komawa zauren majalisar wakilai, amma kuma ana sa ran cimma yarjejeniya game da batun nan ba da jimawa ba.