An yi aringizon kudade a kasafin Nigeria

Tana kasa tana dabo game da aringizon da aka yi wa kasafin kudin Nigeria, lamarin da ya sa kwamitin majalisa ya dage ranar kammala aiki.

A ranar Talata ne kwamitin hadin gwiwa na majalisar dattawan da na wakilai ya sanar da dage lokacin da zai kammala aiki a kan kasafin na shekarar 2016.

'Yan majalisar sun ce hakan ya zama dole saboda abin da suka kira kura-kurai masu yawan gaske da ke kunshe a kasafin.

An dai gano cewa an yi aringizon kudade a kasafin, ga misali Ministan ma'aikatar lafiyar, Isaac Adewole ya ce an sauya baki dayan kasafin da ya bayar.

Sanata Danjuma Goje, shi ne shugaban kwamitin Majalisar dattawa mai kula da kasafin kudi, kuma ya shaida wa BBC cewa fadar shugaban kasar ta amince cewa akwai kura-kurai a kasafin.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Yaki da cin hanci da rashawa na daga cikin manyan abubuwa uku da gwamnatin shugaba Buhari ta yi wa 'yan Najeriya alkawari.

Kuma wasu masana na ganin warware wannan matsala ta aringizo tana da muhimmancin gaske, ganin yadda tattalin arzikin kasar ke cikin mawuyacin hali, ga kuma fatan 'yan Najeriya na ganin an yi musu ayyukan da za su inganta rayuwarsu.