Republican: Wasu karin 'yan takara sun janye

'yan takarar shugabanci kasa na Jam'iyar Republican Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'yan takarar shugabanci kasa na Jam'iyar Republican

Wasu karin 'yan takara na jam'iyar Republican biyu sun janye daga fafatawar da ake yi na neman wanda zai shiga takarar shugabancin Amurka.

Gwamnan jihar New Jersy Chris Christie--da a baya ake sa ran zai kasance na kan gaba-gaba ya janye ne bayan zaben fid da gwanin da aka gudanar a jihar New Hampshire ranar Talata.

Ya kasance na shida ne a baya sosai da Donald Trump wanda ya samu galaba.

A baya dai jagorarar kamfanin Hewlett-Packard, Carly Fiorina wacce ita kadai ce mace a fagen fafatawar a jam'iyar ta janye.