Mai sayar da Aya a Abuja wanda ke kwalliya

Malam Isa mai Aya
Image caption Guntun gatarinka ya fi sari ka bani

A Najeriya, yayin da wasu ke raina yin kananan sana'oi saboda karancin samu, sai ga shi wani mai sana'ar sayar da Aya ya mutunta sana'arsa, abin da ya janyo masa daraja a idon jama'a.

Wakilin BBC Yakubu Liman, ya yi kicibis da wani mai sayar da Aya akan wulbaro a kasuwar Garki international Market da ke birnin tarayya Abuja.

Mutumin mai suna Malam Isa, na yin talla ne sanye da Kwat, da Nakitayil, shirye tsaf tamkar wani ma'aikacin banki ko kuma wata ma'aikatar gwamnati.

Ya shaida wa BBC cewa ya kan sayar da buhun Aya biyu a kowanne wata, da kuma ribar yake kula da iyalansa har ya taimaka wa iyaye da abokan arziki.

Malam Isa yace kayan da yake sanyawa, kan ja hankalin mutane su sayi Ayarsa, wasu ma har kyauta sukan yi ma sa ba tare da sun sayi Ayar ba.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ga hirar su da Yakubu Liman