Masu sarautar gargajiya sun "kadu" da musuluntar Mandela

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar masu rike da sarautar gargajiya a Afrika ta Kudu sun nuna damuwarsu game da musuluntar da jikan Mandela wato Mandla ya yi.

Kungiyar ta shaida wa BBC cewa kasancewarsa Musulmi zai iya shafar yadda zai gudanar da al'adun Xhosa.

Mandla ya musulunta ne a karshen shekarar da ta wuce, kuma an daura masa aure da Rabia Clarke, a wani masallaci da ke Capetown a makon jiya.

Ya gaji mukamin gargajiya na Cif din Mvezo na kabilar Aba Thembu daga kakansa, Nelson Mandela.

Kakakin kungiyar masu sarautar gargajiyar, Cif Mwelo Nonkonyane ya ce "Babu wata matsala don wani basarake ya koma wani addini, amma damuwarmu ita ce ko zai iya sauke nauyin da ke wuyansa a matsayinsa na shugaba."

A al'adance a Afrika ta Kudu akan bukaci masu sarauta su jagoranci bukukuwan tsafi na nuna godiya ga magabatansu, wanda hakan ya kunshi yanka dabbobi da yi wa magabatan addu'a.

Kuma irin wadannan al'adu sun ci karo da addinin Musulunci.

Hakkin mallakar hoto MandlaMandela

Wakiliyar BBC a Johannesburg, Pumza Fihlani ta ce, akwai yiwuwar Mandla ya samu kansa cikin tsaka mai wuya da zai sa ya sabi ko sabon addinin amaryarsa ko kuma talakawansa.

Musuluntar da ya yi zai iya janyo masa matsala, ba wai saboda addinin ba, sai don rashin tabbas da hakan zai janyo a zukatan talakawansa.

Wannan ne dai karo na hudu da Mandla mai shekaru 42 ya yi aure, kuma shi ne karon farko da ya bi al'adun amaryarsa.

Mista Nonkonyane ya ce tun da fari Mandla ya kaucewa al'adunsu, tun da ya auri rabi'a ya kuma karbi al'adunta.

Acewarsa "A al'adar Afrika mace ita ke bin miji, saboda haka lokacin da Rabia ta amince ta auri Mandla, abin da ake tsammani shi ne ta karbi al'adun mijinta."

Babu dai wani daga cikin dangin Mandla da ya halarci aurensa da Rabia, abin da yasa rahotanni suka rinka yayata cewa ba sa farin ciki da auren ne.

Hakkin mallakar hoto AFP Getty