Malami ya kashe malamai shida a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani malamin makaranta ya harbe abokanan aikinsa su shida a lardin Jazan da ke kudancin Saudi Arabia, a cewar jami'an kasar.

Kafafen yada labari na kasar sun ce tuni 'yan sanda suka kewaye wurin da lamarin ya faru.

Hukumomi sun shiga neman malamin, a cewar rahotanni.

Ba kasafai ake samun kashe-kashe irin wannan ba.