Machar ya sake zama mataimakin Kiir

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Riek ya ce ta yiwu ya koma Juba nan da makonni uku domin ya karbi mukamin

Shugaban Sudan ta kudu Salva Kiir, ya sake nada babban abokin hamayyarsa Riek Machar, a matsayin mataimakin shugaban kasa.

Kuma ana kallon wannan matakin a matsayin wata babbar alama ta gagarumin ci gaban da aka samu, a kokarin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a kasar.

Riek dai shi ne mataimakin shugaban kasa na farko bayan kasar ta samu 'yancin kanta a shekarar 2011, kafin Salva Kiir ya tube shi a shekarar 2013.

Tun a karshen shekara ta 2013 ne kuma mayakan da ke goyon Riek suka shiga gwabza fada da sojojin gwamnati.

Kazamin yakin basasar da ya janyo mutuwar dubbannin mutane kuma ya tilasta wa mutum miliyon daya da rabi barin gidajensu.

Mista Riek Machar dai ya yi na'am da nadin da aka masa, a wani bangare na yarjejeniyar sulhun da aka rattaba hannu a watan Agustan bara.