Ana samun karuwar masu cutar Zika a Brazil

Image caption Sauro ke haddasa cutar Zika

Jami'an lafiya a Brazil sun rawaito cewa ana samun karuwar jariran da suke dauke da cutar da ta ke kawo tawaya ga kwakwalwar jariri wadda ake alakantata da Zika.

Ma'aikatar lafiya kasar ta ce yanzu haka an gano jarirai dari hudu da sittin da biyu da aka tabbatar suna dauke da wannan cuta.

Kazalika ana bincike a kan kusan mutane dubu hudu wadanda ake kyautata tsammanin suna dauke da cutar.

Cutar wadda Sauro ke haddasa ta, ta yadu a Latin Amurka fiye da shekara guda.

A yaune dai za a tura sojoji fiye da dubu dari biyu zuwa sassan Brazil, domin su gargadi al'ummar kasar game da illar da cutar da Zika ke da ita.