Masu bata yara na musanya hotuna ta facebook

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption facebook

Masu lalata da kananan yara na amfani da shafinsu na facebook wajen mausanya hotuna a tsakanin junansu.

Wasu na'urori da aka tsara a cikin dandalin facebook na tsare musu sirri ta yanda sai abokan mu'amalarsu ne kadai za su ga abin da suke yi a shafukansu.

Kwamishinar da ke kula da al'amuran yara ta Ingila, Anne Longfield ta ce kamfanin facebook ya gaza wajen sa ido a kan ma'bota dandalin tare da samar da isasshiyar kariya ga yara.

Sai dai jami'in hulda da jama'a na kamfanin facebook ya shaida wa BBC cewa ya dukufa wajen cire abubuwan da ba su dace ba a cikin dandalin.

Wani binciken da BBC ta gudanar ya bankado wasu kungiyoyi da wasu mazaje masu sha'awar lalata da yara suka kirkiro, ciki har da wani mutumin da aka taba kama shi da laifin lalata da yara.

Kuma da ganin sunayen kungiyoyin za ka fahinci cewa manufarsu ita ce lalata da yara, kuma ba makawa sukan kunshi hotunan batsa.