'Yar tsanar Barbie ta zama 'Hijarbie'

Hakkin mallakar hoto Hijarbie

'Yar tsanar Barbie mai sanye da hijabi ta zama tauraruwa a shafin Instagram.

Wata matashiya musulma 'yar Najeriya mai tsokaci a shafin intanet, Haneefah Adam ce ta sauya wa fiticacciyar 'yar tsanar kamani.

Watanni biyu da suka wuce ne matashiyar ta soma sanya hotunan "hijarbie", watau Barbie mai hijabi.

Hakkin mallakar hoto Hijarbie

Haneefah ta gayawa shafin Mic cewa ta samu ra'ayin yin haka ne lokacin da ta yi tunanin "ina son in ga Barbie ta sanya kayan da nima nake sakawa domin in rufe jiki na".

Haneefa ce ke dinkawa kanta hijaban da take saka wa.

Matashiyar mai shekaru 24, ta ce tana aiki domin soma yin 'yar tsanan "hijarbies" na sayarwa.

Hakkin mallakar hoto Hijarbie
Hakkin mallakar hoto Hijarbie

Haneefah ta bayyana cewa tana sha'awar dinka tufafin bakaken Barbie, amma kuma ba ta samun ire-iren su a Najeriya.

A watan da ya gabata, mai hada 'yar tsanan ya bayyana aniyarsa ta fara sauya tsarin jiki da launin fatar Barbie.

Hakkin mallakar hoto Hijarbie
Image caption Haneefah Adam, 'yar Najeriya da ta sauya Barbie

Haneefah dai ta ce za ta iya cusa wa 'yan mata ra'ayin sanya hijabi.

"Wannan zai bayar da damar fadakarwa domin idan kana da kayan wasan da ke daukaka tarbiyya da addinin ka, da kuma tsarin rayuwarka, hakan zai janyo daukaka da mutunta kai," in ji Haneefah.