Syria: za a cimma yarjejeniya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana bukatar ayyukan jin kai a Syria

Kasashen da ke shiga tsakani a rikicin kasar Syria na sa ran cimma yarjejeniyar dakatar da bude-wuta a kasar Syria baki daya nan da mako guda.

Kazalika an daidaita a kan matakan da za a dauka wajen yassare wa al'umomin da rikicin ya ritsa da su ukubar da suke ciki.

Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ne ya sanar da wannan yunkurin, tare da takawaransa na kasar Rasha, Sergei Lavrov da kuma wakilin majalisar dinkin duniya a Syria, Staffan de Mistura.

Ya ce "yau a Munich mun yi amanna cewa mun samu ci gaba a bangaren ayyukan jin-kai da kuma kokarin kashe wutar rikici. Kuma idan aka aiwatar da wannan yarjejeniyar yadda ya kamata, to za ta kawo sauyi mai fa'ida ga rayuwar al'umar Syria."

Mr Kerry ya ce Amurka da Rasha da sauran kasashen duniya na da burin ganin an gaggauta magance rikicin Syria, kuma za su yi aiki tare wajen cimma wannan burin.