Dan Najeriya ya yi kasuwa a India

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

An ba wani dan Najeriya damar nuna bajintarsa a bikin rawa da waka da za a yi a India a watan Maris, a matsayin bako na musamman wanda za a nunawa duniya.

Dan Najeriyar ya yi kasuwa ne a Indiya a wata gasar rawa da waka, a inda ya doke 'yan kasar kimanin 8,000.

Dalibin mai suna Ado Abdulkadir ya na karatu ne a jihar Karnataka da ke kudancin kasar, kuma ya shiga gasar rawa da wakar ne da ake kira Re Ga Ma Pa da harshen Kannada mai wuyar koyo.

A hirar sa da BBC, Ado ya ce sha'awarsa da yaren Indiya ta sa ya kware, har kuma ya koyar da shi a Abuja kafin ofishin jakandancin India a Najeriya ya ba shi damar zuwa karo ilimi a kasar.

Wakilin BBC Yakubu Liman ya yi hira da shi ne a lokacin da wani hoton bidiyonsa yana rawa da waka a gasar, ya bazu a dandalin muhawara da sada zumunta a intanet a watan Janairun shekarar nan.

A hirar da ya sake yi da shi ta dandalin aika sakonni na whatsapp, a ranar Laraba, Ado ya ce an fitar da shi a yayin da suka saura su goma 14.

Bisa tsari ana fitar da mutane biyu ne a duk mako, da haka a cewarsa, ya kai wannan mataki bayan ya kayar da Indiyawa 8,000.

Sannan ya kara da cewa, duk da an fitar da shi, ya burge masu gasar da kuma jama'ar kasar, a dalilin haka ne ma aka ba shi damar sake shiga gasar ba tare da gogayya ba a karo na gaba.