'Mun ceto mutane 45 daga Boko Haram'

Image caption Rundunar sojin hadin gwiwa ce tsakanin Kamaru da Najeria suke ceto mutanen daga hannun 'yan Boko Haram, cikin wadanda aka ceto sun hada da mata da yara

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta ceto mutane 45 daga hannun yan Boko Haram ta kuma sami nasarar kashe goma daga cikin yan kungiyar a wani farmakin hadin gwiwa da takwarorinsu na Kamaru.

Kakakin rundinar sojin Kanar Sani Usman Kukasheka wanda ya baiyana hakan a cikin wata sanarwa ya ce sojoji hudu sun sami rauni yayin da suka bi ta kan nakiyar da aka binne a karkashin kasa.

Mutanen da aka ceto din sun hada da mata 17 da yara 28.

Kanar Sani Kukasheka yace sun farmakin na hadin gwiwa ne domin kakkabe yan Boko Haram daga kauyen Ngoshe da ke kan iyaka tsakanin Najeriya da Kamaru.

Hakan nan kuma sojojin sun lalata wani wurin hada nakiyoyi na yan Boko Haram a kauyen.