Zika: Sojoji za su wayar da kai

Image caption Sojojin za su shiga gida-gida domin wayar da kan jama a kan illar cutar Zika da kuma muhimmancin amfani da gidan sauro

Za a tura sojoji fiye da dubu dari biyu zuwa sassan Brazil, domin su gargadi al'ummar kasar a kan da illar da ke tattare da cutar Zika.

Sojojin za su a rarraba kasidu, za kuma shiga gidajen jama'a su wayar musu da kai a kan yadda za su yaki sauro.

Shugaban kasar Dilma Rousseff ya ce ta hakan ne za a yi maganin cutar har sai an allurar maganinta.

Ma'aikatar lafiya kasar ta ce an gano jarirai 462 da aka tabbatar suna dauke da wannan cuta.

Ana bincike a kan kusan mutane 4,000 wadanda ake kyautata tsammanin suna dauke da cutar.

Cutar wadda Sauro ke haddasa ta, ta yadu a Latin Amurka fiye da shekara guda.