Burundi:Ba za mu yarda da katsalandan ba

Dubban jama'a a Burundi sun bi sahun zanga zangar da ta sami goyon bayan gwamnati wajen yin jerin gwano a Bujumbura babban birnin kasar domin nuna rashin amincewa da abin da suka kira katsalandan din Rwanda a harkokin kasar.

Dandazon jama'a da suka taru a kofar ofishin jakadancin Rwanda sun yi Allah wadai da shugaba Paul Kagame wanda suka baiyana a matsayin makiyin kasar.

Rwanda dai ta musanta zarge zargen baya bayan nan wanda Majalisar Dinkin Duniya da Amurka suka yi cewa ta na horar da yan gudun hijira su kai hari a cikin Burundi.

Daruruwan mutane sun rasu fiye da dubu 250 kuma sun yi kaura a watanni tara da aka yi ana tarzoma sakamakon ayyana yin tazarce karo na uku a karagar mulki da shugaba Pierre Nkurunziza ya yi a watan Aprilun bara.