Nerandra Modi ya kwafsa

Nerandra Modi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shafin Google ya yi kuskuren rana.

Ma'abota shafukan sada zumunta na zamani sun samu abin yin ba'a ga Firayim Ministan Indiya, Nerandra Modi sakamakon wani riga-mallam-masallacin da ya yi wajen taya shugaban Afghanistan, Ashraf Ghani murnar kewayowar ranar haihuwarsa.

Firayim Ministan Indiyan dai ya yi amfani ne da shafinsa na twitter wajen taya Ashraf Ghanin murnar ranar haihuwar tasa, alhali sai nan da wata uku masu zuwa ne ranar za ta zo.

Ganin haka ne Mr Ashraf Ghani ya ba shi amsa, yana cewa sai ranar 19 ga watan Mayu mai zuwa ne ranar za ta kewayo, amma duk haka ya masa godiya, yana murmusawa.

Kuma daga nan ne wani ma'abocin Twittar ya wallafa sakonsa, yana ba'a, cewa yana taya Ashraf Ghani murnar sake haihuwarsa da aka yi.

Nan take wani ya wallafa nasa sakon yana cewa Nerandra Modi ya tabka wannan kuren ne, saboda ya dogara da irin bayanan da ya samu daga intanet.

Shafin "komai da ruwanka" na Google ne ya yi kuskuren sanya ranar 12 ga watan Fabrairu a matsayin ranar haihuwar Mr Ashraf Ghani.