An kashe fararen hula a Afghanistan — MDD

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojiojin gwammnati da na 'yan adawa ne ke da alhakkin mutuwar fararen hula da yawa a Afghanistan, a cewar Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan fararen hular da suka jikkata a Afghanistan sun karu daga kashi hudu a shekarar 2015 zuwa wani kaso mai yawa.

Majalisar ta ci gaba da cewa, fararen hula 3,500 ne aka hallaka, sannan aka raunata 7,500.

Duk da cewa yawan fararen hular da aka kashe sun ragu da kasa da 150 a shekarar 2014, wadanda suka ji munanan raunuka sun karu.

Alkaluman da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar na nuna cewa kashi 62 sojoji masu adawa da gwamnati ne suka raunata su.

Kashi 17 sojoji masu goyon bayan gwamnati ne sanadi, ciki har da sojojin kungiyar tsaro ta NATO.

Yayin da kashi 17 kuwa, musayar wuta ce ta rutsa da su.